1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙalubalantar dokar ta ɓaci a Thailand

April 9, 2010

Magoya bayan tsohon Firaministan Thailand na ci gaba da jerin gwano a Bangkok don nuna adawa da manufofin gwamnati mai ci a yanzu.

https://p.dw.com/p/MrNf
Hoto: AP

Masu zanga - zangar nuna adawa da gwamnatin ƙasar Thailand, sun fara wani jerin gwanonsu a yau juma´a duk da dokar ta ɓaci da hukumomin ƙasar suka kafa. Bayanan da ke fitowa daga birnin Bangkok sun nunar da cewa gungun mutane sanye da jajayen kaya sun nufi wata tashar telebijin da hukumomin suka rufe. A wurare daban daban har goma ne magoya bayan tsohon Firaminista Thaksin Shinawatra suka ƙudiri aniyar gudanar da jerin gwano a ƙasar da nufin tilasa ma firimiya na yanzu sawka daga karagar mulki. Tun a jiya ne masu zanga - zangar suka fara taho mu gama da jami´an tsaro, tare da yin karar tsaye ga zaman majalisar dokokin ƙasar. Wannan dai, ita ce zanga - zanga mafi muni da 'yan adawan ke yi, tun sa'adda suka fara gudanar da jerin gwanon nuna adawa da gwamnatin Abhisit Vejjajiva.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita:Yahouza sadissou