1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarfafa haɗin kan tsaro da al´adu tsakanin Nijeriya da Nijer

Mohammad AwalDecember 11, 2008

Naɗin jakadan Nijer a Nijeriya a matsayin garkuwan wasu jihohin arewa 17

https://p.dw.com/p/GDWE
Taswirar Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja a tsakiyaHoto: AP Graphics

A ci gaba da ƙoƙarin samo ƙwararan hanyoyin ƙarfafa tsaro da zumunci da kyautata al´adu a tsakanin Janhuriyar Nijer da Tarayyar Nijeriya, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Mai Yasin ya naɗa jakadan ƙasar Nijer a Nijeriya Alhaji Ibrahim Musa a matsayin garkuwan masarautun jahohi 17 na gabacin Nijeriya domin ya riƙa haɗa kan sarakuna ƙasashen biyu kan harkokin da suka shafi tsaro da walwalar jama a. Wannan matakin ya samu amincewar ministan tsaro na Nijer. Ana fata wannan sarautar ta garkuwan za ta ƙara zama wata kafar ƙara samun tsaro a tsakanin Nijer da Nijeriya tare da yawaitar arziki da fahimtar juna tsakanin al´umomin ƙasashen biyu.