1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin iko ga ma'aikatan leƙen asirin Rasha

July 29, 2010

Gwamnatin Rasha ta danƙa ƙarin iko ga ma'aikatar leƙen asirinta(FSB)

https://p.dw.com/p/OXiM
Shugaba Vladimir Putin, ta dama, da Framinista Dmitry Medvedev, ta hagu.Hoto: AP

Shugaban Rasha Dmitry Medvedev, ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da ke buƙatar ba da ƙarin iko ga ma'aikatar leƙen asirin ƙasar wato FSB. Fadar mulkin ta Kremlin ta ce wannan doka za ta maido da wani tsari da aka bi a zamanin Tarayyar Soviet na yin kashedi ga duk wanda aka yi imanin cewa yana da aniyar aikata wani mugun aiki. FSB wadda ta gaji KGB ta zamanin Soviet, yanzu tana da hurumin kiran duk wani da ake zaton yana shirin aikata wata ɗanya da ya bayyana a gabanta domin yi mishi gargadi, domin murƙushe duk wani mataki da za a ɗauka da ka iya yin barazana ga tsaron ƙasar. Masu nuna adawa da wannan doka sun ce za a yin amfani da ita domin sa tsoro a zukatan 'yan jarida da 'yan adawa, kuma hakan wani abu ne da ya saɓa wa alƙawarin Medvedev na kare haƙƙin jama'a.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal