1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar sojojin Jamus a Afganistan

April 16, 2010

Mutuwar ƙarin sojojin Jamus huɗu a Afganistan ya tada sabuwar mahaura a fagen siyasar Jamus

https://p.dw.com/p/My3j
Merkel da Zu-Gutenberg na sujuda ga gawawakin sojojin Jamus da suka mutu AfganistanHoto: AP

Yan siyasar Jamus sun fara bayyana buƙatar duba hanyoyin maido sojojin Jamus dake ƙasar Afganistan gida, bayan da dakaru huɗu suka rasa rayuka jiya, a arewacin ƙasar,a yayin da mayaƙanTaliban suka buɗe musu wuta, a lokacin da suke yin sintiri a birnin Baghlan.

 Shugabar gwamnatin gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayana alhini ga wanda haɗarin ya rutsa da su, to saidai duk da haka tace sojojin Jamus zasu cigaba da zama a Afganistan ta bayyana hujja kamar haka:

" Hakan ya zama wajibi ba wai kawai don ceton al´umomin ƙasar Afganistan ba, a´a har ma don kare Jamus da sauran ƙasashen demokraɗiya daga sharrin´yan ta´ada."

Wannan mutuwar dai, ta zo ne sati biyu kacal bayan da wasu sojojin Jamus ukku suma suka gamu da ajalin su, yayin wani kwanton ɓauna da mayaƙan Taliban suka yi musu.

Ministan kula da harkokin tsaron Jamus Karl - Theodor zu Guttenberg, wanda ya kai ziyarar ba zata ga sojojin na Jamus dake aiki a ƙasar Afghanistan ranar Laraba, ya ce, zai sake komawa ƙasar domin sanin taƙameimei abinda ya faru.

 A jiya Larabar ce Guttenberg ya yi alƙawarin cewar, dakarun na Jamus zasu sami manyan tankunan yaƙi da ababen hawa ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita:Umaru Aliyu