1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen taron ƙasashen yankin Sahel a Chadi

July 23, 2010

Taron ƙungiyar CEN SAD a N'Djamena ya amince da manufofin Shugaban Sudan na samar da zaman lafiya

https://p.dw.com/p/OSW2
Hoto: picture-alliance/dpa/Montage DW

 Taron gamayyar ƙasashen yankin Sahel da aka gudanar a birnin N´Djamena na ƙasar Chadi, ya goyi bayan shugaba Omar Al-bashir na ƙasar sudan da kotun hukunta laifuffukan yaƙi ta ƙasa da ƙasa ke zargi da hannu cikin kisan kiyashin da ya auku a yankin Darfur.

A yayin taron, mai masaukin baƙi shugaba Idriss Deby, ya buƙaci shugabannin ƙasashen yankin su marawa ƙoƙarin da ake na tabbatar da zaman lafiya a Sudan, tare da warware rikicin Darfur.

Taron ya nuna ƙin amincewarsa da zarge- zargen da ake yi wa shugaba Al-bashir.

Sakataran zartaswa na Ƙungiyar Mohd Al-Madani Al-Azhar, ya ce waɗannan zarge- zarge ba zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya a yankin na Sudan da ke fama da rikici ba.

Akan haka ne ya ce, ƙungiyar da ta ƙunshi ƙasashe 13 na ba da cikakken goyon bayanta ga Sudan da al'ummarta.

Tarayyar Turai da Ƙungiyoyin kare haƙƙin biladama , sun yi suka ga ziyarar da Al-bashir ya kai Chadi, wadda tana ɗaya daga cikin ƙasashen da su ka aminta da kotun hukunta laifufukan yaƙi ta ƙasa da ƙasa, amma kuma ta ƙi bin umarnin kotu na kama shugaba Albashir.

mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Yahouza Sadissu Madobi