1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙarshen taron Brazaville a game da cutar Sida a Afrika

March 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5U

An birnin Brazaville na ƙasar Congo, an kammala zaman taron yini 3, da ya haɗa ƙurraru ta fannin kiwon lahia, da su ka hito daga kasashe 53 na Afrika, da hukumar yaƙi da cutar Aids ta Majalisar Ɗinkin Dunia.

A tswaon wannan kwanaki sun tantana a kann halin da ake ciu ta fannin yaki da cutar Sida a Afrika.

Bayan masanyar ra´ayoyi ,sun cimma matsaya ɗaya a kan cewar, cutar na ƙara bazuwa kamar wutar daji duk da ƙoƙarin da ake na magance ta.

Sanarwar ƙarshen taron, ta gayyaci ƙasashen Afrika, su ƙara matsa ƙaimi ga yaƙi da wannan cuta, ta fannin lumka yawan kuɗaɗe, da kuma ƙalailaice cewar,an yi amfani da wannan kuɗaɗe ta hanyar da ya dace.

Taron ya yi kira, ga shugabanin ƙasashen Afrika, da su cika alƙawuran da su ka ɗauka, a taron Abujar Nigeria, a shekara ta 2001, inda su ka ce, a nan gaba kashi 15 bisa 100,na jimmilar kuɗaɗen da kasashen su ka mallaka, a za a saku ta fannin ayyukan kiwon lahia.

Daga ɗaukar wannan alkawari zuwa yanzu, ƙasashe 2 rak, su ka cika wannan alkawari, bisa manufa, inji shugaban hukumar kiwon lahia ta Majalisar Ɗinki Dunia a jawabin sa na ƙarshen taro.