1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen taron ECOWAS a Abuja

June 15, 2006
https://p.dw.com/p/Butv

Shigi da ficin makamai nna ɗaya, daga mahimman batutuwan da shugabanin ƙasashen ƙungiyar Ecowas kokuma Cedeao,su ka tanttana jiya, a taron da su ka gudanar a Abujan Nigeria.

Sanarwar ƙarshen taron ta bayana haramta shigi da ficin makamai, tsakanin ƙasashe 15 membobin ƙungiyar, muddun ba ƙasashen ba,su ka cimma yarjejeniya, ta fitar ko shigar da makamai, a ɗaya, daga cikin su, dalili da tsaro.

Kazalika, shugabanin sun cimma daidaito, a kan ɗaukar matakin ƙarfaffa sapara makamaai a iyakokin su.

Cedeao ta ɗauki wannan mataki, da zumar kawo ƙarshen faɗace-faɗace, da a ke fuskanta, nan da cen.

A share ɗaya kuma, shugabanin ƙasashen Ecowas, sun yanke shawara cenza tsarin gudanarwar na ƙungiyar.

Sun girka wata hukuma da ta ƙunshi ƙasashe 9, wace za maye gurbin opishin zartaswa mai aiki yanzu, daga watan Janairu na sabuwar shekara.

An kuma baiwa ƙasar Ghana, jagorancin wannan hukuma.