1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙarshen taron majalisar wakilai a China

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv58

Yan majalisar wakilai 3000, na ƙasar China, sun kammalla zaman taron majalisa, na shekara banna.

Tare da gagaramin rinjaye, sun bayyana amincewa, da daftarin tafiyar da ayyuka, da gwamnatin Pramista Wen Jiabao, zata gudanar, a tsawan shekaru 5 masu zuwa.

Wannan daftari, ya ƙunshi rage giɓin bambancin rayuwa, tsakanin mazauna birane, da al´ummar karkara, da ke fama da matsanancin talauci.

Da kuma ƙara yawan kuɗaɗe, don haɓɓaka albarkatun noma.

Kazalika, yan majalisar wakilan, sun amince da ƙara yawan kassafin kuɗi, da gwamnati ke sakawa ta fannin harakokin soja.

A ɗaya hannun kuma, sun tabka mahaurori masu zafi, a game da batun tattalin arziki, da cinikaya tsakanin, China da ƙasashen dunia.