1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen ziyara Georges Bush a ƙasar Pakistan

March 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bv60

Shugaba Bush na Amurika ya kammala ziyara aikin da ya kai a ƙasar Pakistan.

A ganawar da yayi da shugaba Pervez Musharaf, sun tantanana a game da batutuwa da su shafi yaƙi da ta´adanci, da kuma wajibcin ƙara ƙarffafa mulkin Demokadiyya.

A wani taron manema labarai day a kira ,Bush ya jinjina damtsen shugaban Pakistan, a kan hadin da ya ba Amurika, a gwagwarmayar da ta ke, na yaƙi da ta´adanci.

Sannan ya yaba kokarin da hukumominPakistan da na India su ke ta fanning warware rikicin yankin Kashemir.

Saidai , rahotani sun nunar da cewa, saɓanin ƙasar India, inda Bush ya kamalla ziyara jiya, a Pakistan ba a cimma wata yarjejeniya ba, ta ɓangaren nulkea.

Ida na ba manta ba, a jiya,Bush da hukumomin New Dehli, sun rattaba hannu, a kan wata yarjejeniya , ta fannin makamashin nulkea, da yawan kuɗaden ta, su ka kai dalla billiard 20.

Albarakacin wanan ziyara da shugaban Amurika ya kai Pakistan,dubun dubanan jama´a, a birane daban-daban na Kasar, sun shirya zanga zangar nuna ƙyamar Amurika da shugaban ta.

A Islamabad babban birnin Kasa Pakistan, hukumomi sun ɗauki tasatsauran mattakan tsaro, don riga kafi ,ga hare haren ta´adanci, irin wanda su ka wakana, ranar alhamis da ta wuce, a ƙaramin opishin jikadancin Amurika, da ke Karaci.