1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen ziyara Tony Blair a Afrika

June 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuK5

Praministan Britania Tony Blair, ya kammalla ziyara bankawana a nahiyar Afrika, inda a yau ya gana da hukumomin Afrika ta Kudu.

Blair da Tabon Mbeki, sun tantanana a game da al´ammura daban-daban, da su ka shafi diplomatia da kuma cinikaya, tsakanin London da Pretoria.

Kazalika, sun yi anfani da wannan dama, domin masanyar ra´ayoyi a kan rigingimun da ke gudana a Afrika, mussamman a ƙasar Zimbabwe.

Tony Blair, ya yi kira ga ƙasashen Afrika,su da kansu, su gano bakin zaren warware rikicin siyasar da ke wakana a ƙasar Zimbabwe, sannan ya yi yabo ga Tabon Mbeki, a game da kyaukyawar rawar da ya ke takawa, domin kawo ƙarshen wannan rikici.

Tony ya alkawarta shigewa Afrika gaba, wajen takwarorin sa na G8, domin su dubi matsalolin talaucin Afrika da idon Rahama.

Nan gaba a yau ne Tony Blair, zai tashi zuwa birnin London.