1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

171110 D Terrorgefahr

November 18, 2010

An tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa a Jamus

https://p.dw.com/p/QCcN
Ɗaya daga cikin 'yan sanda ɗauke da bindiga dake gadin filin jirgin saman birnin FrankfurtHoto: AP

A wani taron manema labarai a birnin Berlin ministan cikin gida Thomas de Maiziere ya ce sabbin bayanai da suka samu daga wajen ƙasar sun tabbatar da cewa masu tsattsauran ra'ayin Islama na shirin kawowa Jamus ɗin harin ta'addanci a ƙarshen wannan wata na Nuwamba.

Ministan cikin gidan Tarayyar Jamus Thomas de Maiziere ya faɗawa taron manama labaran cewa ana da dalilin nuna damuwa amma ba bu wani dalili na ɗimauta.

Kawo yanzu ministan bai taɓa ba da tabbacin yiwuwar kawowa Jamus harin ta'addanci ba. Ya ce an samu sahihan bayanai daga ƙetare dake nuna cewa an yi shirin ƙaddamar da harin ta'addanci a ƙasar a ƙarshen watannan na Nuwamba, kuma waɗannan bayanan sun yi daidai da sabbin bayanan sirri na jami'an tsaron cikin gida. A saboda haka halin da ake ciki ya canza, musamman game da sabbin matakan tsaro.

"Na umarci rundunar 'yan sanda da ta ɗauki sabbin matakan tsaro mafi dacewa da wannan sabon hali na barazana da muka shiga musamman a filayen saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa. Za a ci-gaba da ɗaukar waɗannan matakan har sai abin da hali yayi."

Bugu da ƙari an kuma umarci 'yan sandan jihohin ƙasar da su ƙara ba da kariya ga wuraren da tun a da ake ganin suna iya zama wuraren da za a iya kaiwa hari.

Ministan ya ce a kwanakin nan dake tafe jama' a za su ga matakan tsaron na 'yan sanda to amma akwai wasu da dama da ba za su iya gani ba.

A cikin wani gargaɗi da ya yi kimanin makonni biyu da suka wuce ministan cikin gidan yayi kira ga jama'a da su ƙara hattara kana kuma su sanar da 'yan sanda duk wani ƙunshi ko wani abin da suka gani da ba su amince da shi ba.

"Ko da yake bayanan da muka samu sahihai ne, amma ba dalili ba ne kuma ma bai kamata su zama wata hujjar sauya tsarin rayuwar al'umma gaba ɗaya ba. Yin haka kamar wani kuskure ne, kuma abin da 'yan ta'addan ke so kenan."

Biyowa bayan gargaɗin na barazanar harin ta'addancin a Jamus, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta 'yan sanda Konrad Freiberg ya soki lamirin gwamnati da rashin zama cikin shirin tinkarar wani hari da za a iya kaiwa ƙasar. Ya ce tun ba yau ba 'yan sanda sun nunawa hukumomin wuraren da ake da rauni na tsaro.

A halin da ake ciki ministan cikin gidan ya ce Jamus da ƙasashe maƙwabtanta da kuma ƙawayenta sun ƙarfafa tuntuɓar juna tsakani kana ƙasar ta tsaurara matakan tsaro akan iyakokinta. Hakan dai na nuna cewa wataƙila har yanzu masu shirin kawo harin suna wajen ƙasar ta Jamus.

Mawallafa: Peter Stützle/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas