1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300810 Irak USA

August 30, 2010

A watan Satumba, sauran sojoji dubu 50 da suka rage a ƙasar masu horad da jami'an tsaron ta, suma za'a kwashe su daga Irak.

https://p.dw.com/p/OzfZ
Hoto: AP

Runduna ta ƙarshe dan Amerika tun a ranar 19 ga watan Agusta ta fice daga ƙasar ta Irak. A watan Satumba, sauran sojoji dubu 50 da suka rage a ƙasar masu horad da jami'an tsaron ta, suma za'a kwashe su daga Irak. Gobe Talata, shugaba Barack Obama zai sanar da cewar Amerika ta kawo karshen yakin da Amerika tayi a Irak. To sai dai shekaru bakwai bayan kawar da gwamnatin Saddam Hussein, kasar bata kusanci samun abin da za'a kwatanta shi da zaman lafiya ba.

Ina maku murna kun tafiyar da aikin ku da kyau. Ina fatan zaku koma kasar ka lafiya, ku kuma sadu da iyali da yan uwa da abnokan arziiki lafiya.

Wannan dai muryar wnai mutum ne dake sallama da sojojin Amerika da suka yi yaki a Irak a birnin Bagadaza. Aikin da aka baiwa sojojin dai ya kare, runduna ta karshe tun misalin makonni biyu da rabi da ska wuce ta janye daga ƙasar ta Irak. Sauran sojojin Amerika dubu 50 da zasu rage a ƙasar, duka mashawarta ne da masu aikin horad da jami'an tsaron Irak, ba tare da an basu izinin shiga faɗa ko yaƙi ba. Da ɗin ma a karshen shekara mai zuwa za'a janye su. Shugaban Amerika Barack Obama yace:

Irak Doppelbombenanschlag Zwillingsbomben Baghdad
Hoto: AP

"Ba zamu ci gaba da sintiri har abada a kan titunan Irak ba, har sai mazauna kasar sun tabbata masu cikakken tsaro, ba kuma zamu ci gaba da zama kasar ba har sai ta kai ga tabbatarda cikakken hadin kanta."

Tun daga yanzu, ƙasar ta Irak mai arzikin man fetur, amma wadda yaki yayi kaca-kace da ita, an kyale ta, ta nemi yadda zata daidaita kanta da halin da ake ciki a al'amuran gabas ta tsakiya. Shi ko zata sami nasarar hakan. Abdel Bari Atwan, babban editan jaridar nan mai suna Al Qus al-Arabi yace bai hangi wani haske ba game da makomar ƙasar ta Irak.

Yace a zato na, ƙungiyar al-Qaeda zata sake kmawa cikin ƙasar. Irak dai ta kama hanyar shiga cikin hali na ruɗani da tashin hankali mai tsanani, wanda a sakamakon hakan ƙungiyoyi da suka fi al Qaeda tsanani ma zasu ɓullo.

Atwan yace wannan ra'ayi nashi ya kara samun karfi idan aka duba hare-haren baya-bayan nan. A watan Yuli kadai, bisa kididdigar hukumomin Irak, mutane 535 ne suka rasa rayukan su a sakamakon harin bama-bamai, wanda shine adadi mafi yawa a tsakanin fiye da shekaru biyu. Amerikawa sun zuba jari mai yawa a aiyukan horaswa da daura damarar makamai da kayan aiki ga rundunar yan sanda da soja da hukumar leken asirin Irak.

Barack Obama Columbus Ohio USA
Hoto: AP

Mataimakin shugaban Amerika, Joe Biden yana koƙarin matsa lamba ga duk masu ruwa a halin da ake ciki a Irak, amma bai sami nasara ba.

Ya ce ni da kaina na nunawa shugabannin siyasa na Irak cewar lokaci yayi da zasu ɗauki nauyin jama'a da ya kamata ya kasance a kansu, ta hanyar fara ɗaukar matakan neman kafa gwamnati.

Sai dai kuma ko wane jami'in siyasa na Irak yana da magoya bayan sa a ketare. Ɗan siyasar da ya sami nasarar zaɓen da aka yi, wato Iyad Allawi yana samun ɗaurin gindin Turkiya da Amerika da Saudi Arabia. Abokin adawar sa Nuri al-Maliki yana samun goyon baya daga Iran. Hakan ya kara rikirkita al'amura.

Kasawar yan siyasar Irak kuma ya zama abin farin ciki ga ƙungiyoyi na yan ta kife a ƙasar. Waɗannan ƙungiyoyin sukan maida hankalin su ga daukar yan Irak masu fama da rashin aikin yi. Waɗanda yawancin su matasa ne da basa hangen haske ko wata makoma mai armashi ga rayuwar su a Irak.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar