1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Erythrea ta janye daga IGAD

April 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuN8

A yau lahadi ne,ƙasar Erythrea, ta bayyana jayewa daga ƙungiyar haɗa kan ƙasashen yankin ƙafon Afrika, da na gabacin nahiyar wato IGAD.

Hukumomin Asmara, sun ɗauki wannan mataki , dalili da abinda su ka kira „shiga sharo ba shanu“ da ƙasar Ethiopia ta yi, a rikicin kasar Somalia, ba tare da ƙungiyar IGAD, ta ce uffan ba.

A yanzu hada dai akasar ta Somalia a na ci daga da ɓarin wuta tsakanin dakarun gwamnati ,masu goyan bayan EThiopia, da kuma baradan kotunan Islama.

A cewar ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, da ke birnin Mogadiscio, a ƙalla mutane 55 su ka rasa rayuka, tsakanin jiya da yau, a cikin wannan arangama.