1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Estoniya za ta fara yin amfani da takardar kuɗin Euro

July 13, 2010

A ranar ɗaya ga watan Janairu na shekara 2011 ƙasar Estoniya za ta fara amfani da kuɗin Euro

https://p.dw.com/p/OIEd
takardun kuɗin EuroHoto: dpa/PA

Ministocin kuɗi na Ƙungiyar Tarayyar Turai sun amince da ƙasar Estoniya ta fara yin amfani da takarda bai ɗaya ta kuɗin Euro a farkon sabuwar shekara mai shirin kamawa.

Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe ga ƙasar ta Estoniya na zamewa memba dindindin a cikin Ƙungiyar Tarayyar Turai.

Ƙasar wacce ke a arewa maso gabacin Tarayyar Turai ta shigo ne a cikin ƙungiyar tun a shekara ta 2004, bayan da ta ɓalle daga Tarayyar Soviet a shekara ta 1991, kuma ita ce ƙasa ta 17 a nahiyar ta Turai da za ta yin amfani da takardar kuɗin Euro .

Mawalafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Ahmad Tijani Lawal