1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Qatar na ba da ƙimi wajen inganta harkokin ilimi

YAHAYA AHMEDJuly 18, 2006

A wannan karon, za mu waiwayi yankin ƙasashen larabawan Gulf ne, inda za mu ya da zango a kasar Katar. Ita dai wannan ƙasar na ɗaya daga cikin ƙashen yankin na Gulf masu arzikin man fetur. A ƙasashen yamma kuma, ana yabon sarkin ƙasar Sheikh Hamad Bin Khalifa Bin Thani, tamkar ɗaya daga cikin shugabannin ƙasashen musulmi masu sassaucin ra’ayi, kuma masu hangen nesa da neman ci gaban al’ummansu.

https://p.dw.com/p/BvTS
Tutar ƙasar Qatar
Tutar ƙasar Qatar

Ana yabon sarkin Qatar, Sheikh Hamad Bin Khalifa Bin Thani ne da taka muhimmiyar rawar gani wajen kafa gidan talabijin nan al-Jazeera, wanda a halin yanzu ake gani kamar juyin juya hali ne a fagen yaɗa labarai a ƙasashen larabawan.

A fannin ilimi kuma, ƙasar ta Qatar na kan gaba a jerin ƙasashen labawa. Mahukuntan ƙasar na da ra’ayin cewa, kyautata ilimi zai iya kasancewa wata gada ta haɗe al’adu daban-daban da ke ƙasar.

A taƙaice dai kasar ta Katar, wato wata makurɗaɗa ce da ke cikin tekun Golf. Kuma tun cikin 1971 ne ta sami ’yancinta. Yawan al’ummanta bai kai miliyan ɗaya ba. A halin yanzu ma, an ƙiyasci cewa baƙi da ke zaune ƙasar, mafi yawansu ma’aikata daga nahiyar Asiya, sun fi ’yan ƙasar da kansu yawa. Gano man fetur da aka yi a ƙasar na kimanin garwa biliyan 15, ya sa Katar ta sami bunƙasar tattalin arziki matuƙa. Sarkin ƙasar, Sheikh Hamad Bin Khalifa Bin Thani, bai ɓata lokaci ba, wajen yin amfani da arzikin da ƙasar ke samu daga man fetur da hayaƙin Gas, wajen ginata don ta dace da bukatun zamani.

Abdul Jalil Lahmanate, wani ɗan hannun daman gidan sarautar Katar ɗin ne. Shi ne dai ke kula da wata gidauniyar da uwar gidan sarkin ta kafa don inganta harkokin ilimi da kimiyya da kuma jin daɗin jama’a. A ganinsa, ƙasar ta Katar ƙarama ce kamar Luxemburg, ko Taiwan ko kuma Singapore. Amma tana taka muhimmiyar rawar gani a harkokin yankin na Golf. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„A cikin shekaru 30 zuwa arba’in nan gaba, za a iya samun wani yanayi, inda duk ƙasashen yankin ba su da iyaka kuma. Duk an haɗe an zama ɗaya. Tanadin da Katar ke yi da arrzikinta, zai bai wa al’ummanta damar samun ingantaccen ilimi, sa’annan kuma za su iya taka muhimmiyar rawar gani wajen samad da zaman lafiya da inganta ma’ammala tsakanin al’umman yankin gaba ɗaya.“

Wani ba’Amirke, Patrick Ludwick, wanda ke kula da fannin hulɗa da jama’a na gidauniyar ta Katar ya ba da ƙarin haske kan gidauniyar da kuma aikin da take yi:-

„Tun fiye da shekaru 10 ne dai ke nan da aka kafa gidauniyar ta Katar. Mafi yawan kuɗaɗen shigarta kuma, tana samo su ne daga wata rijiyar haƙo mai, wadda akka keɓe mata musamman, don ta iya gudanad da ayyukanta. An dai yi wa rijiyar laƙabin tushen ilimi. A ko wace rana ana haƙo kimanin garwa dubu 6 daga wannan rijiyar.“

Da kuɗaɗen da gidauniyar ke samu ne te kafa cibiyoyin yaɗa ilimi mai zurfi. Ɗaya daga cikin waɗannan cibiyoyin ne jami’ar nan da aka yi wa suna „birnin Ilimi“ ko kuma „Education City“ a turance, wanda aka gina a bakin teku a yammacin birnin Doha, babban birnin ƙasar. Game da tsarin wannan jami’ar dai, Patrick Ludwick, ya bayyana cewa:-

„A wannan jami’ar, akwai rassan manyan jami’o’in Amirka guda biyar, wato Jami’ar Commonwealth ta al’adu ta Virginia, da Jami’ar ilimin siyasa da shari’a ta Georgetown, da jami’ar Carnegie Mellon ta ilimin injuna masu ƙwaƙwalwa, da jami’ar Texas A & M ta sabbin fasahohi da ƙere-ƙeren injuna, da kuma jami’ar Well Cornell ta koyar aikin likita.“

Duk da cewa dai gidauniyar ce ke ɗauke da nauyin tafiyad da harkokin jjami’ar, ba kyauta ake koyarwa ba. Duk ɗaliban da ke karatun a jami’ar, suna biyan kuɗin karatunsu. Sai kaɗan da bas u da hali ne ake ba su sikolaship. Ana kyautata zaton cewa, kafin shekara ta 2010, yawan ɗaliban jami’an zai kai dubu 20.

A jami’ar dai, mafi yawan malaman da ke koyarwa baƙi ne daga ƙasashen yamma. Akwai dai shhirn maye gurabansu da malaman ƙasar ko kuma daga wasu ƙasashen larabawa. Amma hakan zai ɗau wani lokaci mai tsawo, inji Dr. Abdel Jalil:-

„Birnin Ilimi dai kamar wani tsibiri ne, inda al’adu daban-daban ke cuɗanya da juna, inda kuma ake ta ƙara samun damar tuntuɓar juna. Hakan dai bai sha bamban da al’adunmu na islama ba. A lokacin da da can ma, irin wannan salon ne ya janyo tuntuɓa tsakanin duniyar larabawa da na musulmi da nahiyar Turai.“

Yussif Fahro, shi ma wani ma’aikacin gidauniyar Katar ɗin ne mai kula da hulɗoɗinta na ƙasa da ƙasa. Shi ma ya yi imanin cewa, gudanad da shawarwari da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi ilimi da kimiyya, za su iya taimakawa ƙwarai wajen inganta halin rayuwar jama’a. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Idan muna son mu zauna da juna cikin lumana, to ya kamata mu yarje kann ra’ayi ɗaya. Wato ba harshe ɗaya kamar Turanci ko Larabci ko Spanisanci ba. A’a. Harshen da ya kamata mu yi amfani da shi, shi ne na yaɗa ilimi, da faɗakad da kai. Kamata ya yi mu san yadda za mu yaɗa ilimin da muka samu ga ’ya’yanmu, don su ma a lokacinsu, su samad da kyakyawar yanayi na lumana a duniya baki ɗaya.“