1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashe nawa ne daga nahiyar Afirka suke da ofishin jakadanci a ƙasar Jamus

November 12, 2007

Bayani akan yawan ƙasashen da suke da ofishin jakadanci a Jamus

https://p.dw.com/p/CAVS

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Maidawa: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Halima Buhari daga jihar Jigawa a tarayyar Najeriya. Malamar tana tambaya ne game da cewar, wai shin Ƙasashe nawa ne daga nahiyar Afirka suke da ofishin jakadanci a ƙasar Jamus?

Bashir: To daga cikin ƙasashen da ke nahiyar Afirka, Ƙasashe 24 ne suke da ofishin jakadanci anan Jamus. A ɗaya ɓangaren, Jamus tana da ofishin jakadanci a Ƙasashe 148 a fadin wannan Duniya tamu, amma daga cikin wannan adadi, Ƙasashe 39 ne a nahiyar ta Afirka Ƙasar ta Jamus take da ofishin jakadanci a cikinsu.

Ƙasashen dake nahiyar Afirka sun samu ci gaba ƙwarai sakamakon wannan alaƙa ta jakadanci da Ƙasar Jamus, domin nahiyar ta Afirka ita ce nahiyar da Ƙasar ta Jamus ta fi mayar da hankali akai wajen gabatar da ayyukan ci gaba. Ƙididdiga ta nunar da cewa ƙasar ta jamus aƙalla tana samar da Euro miliyan 3000. Har ila yau bayanai sun tabbatar da cewa, ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ta nan Jamus ta bayar da taimakon raya ƙasa ga Ƙasashe dake nahiyar Afirka, na akalla Euro miliyan 30 a shekara ta 2006.

Idan aka koma ga ɓangaren tattalin arziƙi kuwa sai a ce dangantakar Jamus da Afirka tana ƙara haɓaka ƙwarai da gaske tsawon shekaru da dama. A shekara ta 2006 kaɗai yawan cinikayya tsakanin Jamus da Ƙasashen Afirka ya ƙara bunƙasa da kashi 18 bisa 100, wanda hakan ya mayar da yawan kuɗin cinikayyar zuwa Euro miliyan 33,000. Daga cikin waɗannan kuɗaɗe jarin da Jamus ta saka kaitsaye ya kai Euro miliyan 6000.

A ƙokarin da nahiyar Afirka take yi na haɗewa a matsayin Tarayyar Afirka, Ƙasar jamus tana bayar da gagarumar gudun mowa kwarai- da-gaske, dangane da haka ne ma, Jamus a karkashin gudun mowar shugaba Hoerst Koeler, aka samar da kungiyoyin taimako guda 32 wadanda suke yin aiki tuƙuru wajen wayar da kai da kuma ilimantarwa game da mahimmancin samar da Tarayyar Afirka. Ya zuwa yanzu Jamus ta ƙirƙiri shirye-shirye guda 5000 a nahiyar Afirka, abin da ya kama daga Makarantu zuwa Asibitoci.