1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen dunia na cigaba da Allah wadai ga Corea ta Arewa

Yahouza S.MadobiJuly 5, 2006

Bayan harba makamai masu lizzami Corea ta Arewa na shan suka daga sassa daban daban na dunia.

https://p.dw.com/p/BtzP
Hoto: AP

Cemma dai Hausawa kan ce wai, na san a rina, domin tun a shekara ta 2002 Corea ta Arewa ta hidda hannuwan ta daga yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta hanna yaƙuwar makamai masu guba, sannan, a watan november da ya gabata, hukumomin Corae ta Arewa su ka ƙauracewa tebrin shawara, tare da ƙasashe masu shiga tsakanin wannan taƙƙadama, wanda a tsawan shekaru 3, su ka kasa ciwo kann hukumomin Pyong Yang, na suyi watsi da aniyar ƙera makamai masu lizzami.

Hukumomin sun cigaba da yin baraznara, mallakar makaman nuklea, da kuma masu lizzami.

Wanda su ka harba jiya, a matsayin gwaji, sun haɗa da samparin Taepodong -2, masu dogon zango, wanda za su iya cimma kilomita kussan dubu 7, wato har zuwa yankunan Alaska, kokuma Hawai a ƙasar Amurika.

ƙasar Japon na ɗaya daga sahun ƙasashen da su ka fara maida martani, ga wannan al´amari.

Praminista Yunichiro Koizumi ya ce,Japon za ta ɗauki matakin da ya dace, a lokacin da ya dace, tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Dunia, komu mataki na gaban kanta.

A matsayin somin taɓi, tunni hukumomin Japon, sun umurci wakilan jikadancin Corea ta Arewa, su tattara ya na su ya na su su fita daga ƙasar Japon ba da ɓata lokaci ba.

Sannan kuma, sun haramtawa jiragen samar Corea ta Arewa,zirga zirga, a sararin samaniyar Japon.

Saidai duk da wannan matakan gaggawa, Praministsa Koizumi, ya ce a shire ya ke, ya sake komawa tebrin shawara a kan batun, domin ta hanyar tantananawa kaɗai, za a iya gano bakin zaren warware wannan rikici.

Ƙasar Amurika na cikin shagulgullan sallar ranar samun yancin kai, ta samu labarin harba makaman masu lazzamin da Corea ta Arewa ta yi.

Bada wata wata ba, shugaba Georges Bush ya nuna matuƙar ɓacin rai.

Shima Jikadan Amurika, a Japon Thomas Schiffer, kira yayi ga hukumomin Corea ta Arewa::

Jawabin mu shine cewar wannan al´amari, na matsayin tsokanar faɗa.

Mu na fatan za su daina.

Domin wannan ba mataki ne,wanda zai haifar masu, ɗa mai ido ba, a fagen diplomatia na dunia.

Abunda su ka aikata, na cike da haɗari, kuma zamu ci gaba da tuntunɓar juna tare, da abokan hulɗoɗin mu, domin duba matakan ɓulloma matsalar.

Ƙasashen Rasha,France da Britania, sun bayyana damuwa a dangane da batun, wanda babu shaka a cewar su, zai ƙara dagulla harakoki a yankin baki ɗaya.

A nata ɓagaren ƙasar China, mai nuna goyan baya ga hukumomin Corea ta Arewa, ta bayyana zullumi na fatar baka, ta kuma gayyaci ƙasashen dunia, da su daina ƙarin gishiri ga matsalar, su kuma yi tunani cikin nutsuwa , kamin su maida martanin da su ka ga ya dace.

Sanarwar da opishin ministan harakokin wajen ƙasar China ya hido, ta ƙara da cewa: ɗaukar matakan soja a kan Corea ta Arewa za su ida tada hasumi a yankin.

A nasa ɓangare, Praministan Australiya John Haward, ya bayana ra´ayin ƙasar sa, da cewa:

Abunda Corea ta Arewa ta aikata tamkar, ta burmawa kanta wuƙa ne.

Ina mai fatan dukan ƙasashen da ke iya taka rawa domin magance wannan matsala su kawo gudun muwa, mussamman ƙasashen Japon da China, wanda su ka fi ƙima da ƙarfin faɗa a ji, Corea ta Arewa.

Ita ma hukumar zartaswa ta ƙungiyar gamayya turai, da kuma ƙungiyar tsarom, ta NATO, sun yin tofin Allah tsine, ga hukumomin Pyong Yang a kan harba wannan makamai masu lizzami.