1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen duniya na ci gaba da yi wa Korea Ta arewa kakkausar suka game da gwajin makaman nukiliya da ta yi.

October 9, 2006
https://p.dw.com/p/BugU

Bayan sanarwar da Korea Ta Arewa ta bayar, ta yin gwajin makaman nukiliya a karo na farko a tarihinta, gwajin da kuma ta ce ya sami gagarumin nasara, ba tare da malalar hayaƙin dattin nukiliya mai guba ba, ƙasashen duniya sun yi ta sukar wannan gwajin da Korean ta yi. A cikin wani jawabin da aka buga a birnin Berlin, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya ce ƙasar Korea Ta Arewa tana yi wa kanta saniyar ware, da yin gwajin.

A birnin Brussels kuma, Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, ita ma ta yi kakkausar suka ga wannan gwajin. Da yake ba sanarwa kan matsayin da Ƙungiyar ta ɗauka, babban jami’inta mai kula da harkokin ƙetare, Javier Solana ya bayyana cewa.