1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen EU sun cimma yarjejeniya ta sassuta sufurin jiragen sama

April 19, 2010

Ministocin sufuri na EU sun amince da sassuta tarnaƙi akan zurga zurgar jiragen sama a nahiyar turai.

https://p.dw.com/p/N0be
Ministan sufuri na ƙungiyar EU Siim KallasHoto: AP

Ministocin sufuri na ƙasashen tarayyar Turai sun cimma yarjejeniya ta sassauta tarnaƙin da aka sanya akan zurga zurgar sufurin jiragen sama a nahiyar sakamakon gajimaren toka daga ƙasar Iceland. Ministan sufuri na ƙungiyar tarayyar Turan Siim Kallas ya shaidawa manema labarai bayan tsawon saoí da Ministocin suka yi na taron gaggawa ta hanyar Video cewa daga ranar Talata zaá sami jirage da zasu fara yin jigila. Kwanaki biyar kenan a jere ana soke tashi da saukar jiragen sama a nahiyar turai. A halin da ake ciki hukumar sufurin jiragen sama ta nan Jamus ta bada sahalewa ga kamfanin jiragen sama na ƙasar wato Lufthansa cewa daga ranar Talata ya cigaba da kwaso fasinjoji 15,000 waɗanda suke jiran dawo da su gida. Kamfanin yace zai yi sawu hamsin don kwaso fasinjojin daga arewaci da kudancin Amirka da Afirka da kuma nahiyar Asia.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala       

Edita : Umaru Aliyu