1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen yamma na ta ƙoƙarin kwashe ’yan ƙasarsu daga Lebanon.

July 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bupx

Dubban ’yan ƙasashen ƙetare na ta yunƙurin yin ƙaura daga Lebaon, a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke gargaɗin cewa, halin da ake ciki a ƙasar za ta iya zamowa wata mummunar annoba ga bil’Adama. Tuni dai, hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebaon ɗin sun tilasa wa mutane fiye da rabin miliyan tashi daga matsugunansu.

A birnin Beirut, ɗaruruwan Amirkawa, sun taru gaban ofishin jakadancin ƙasarsu, inda za a kwashe su zuwa tashar jirgin ruwan birnin, don fid da su daga Lebanon ɗin da jiragen ruwan yaƙin rundunar sojin ƙasarsu.

A jiya ne kuma, wani jirgin ruwan yaƙin Birtaniya ya kwashi ɗaruruwan ’yan ƙasar daga Beirut zuwa tsibirin Cyprus, inda rahotanni suka ce ya isa yau da safen nan. Tuni dai, Jamus ta kwaso ’yan ƙasarta kusan su ɗari 3 daga Lebanon, waɗanda suka iso birnin Düsseldorf jiya da safe. Wata sanarwar gwamnatin tarayya da aka bayar a birnin Berlin ta ce, ana shirin kwaso duk Jamusawan da ke zaune a Lebanon ɗin, a cikin ’yan kwanaki nan.