1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙazamin faɗa tsaknain yanTaliban da da rundunar NATO a Afghanistan

September 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuBX

A ƙasar Afghanistan a na ci gaba da ba ta kashi, tsakanin yan taliban da dakarun rundunr ƙasa da ƙasa ta NATO.

Rahottani daga birnin Kaboul, sun nunar da cewa, a ƙala mutane 56 su ka rasa rayuka, a cikin faɗa mafi muni da ɓangarorin 2 su ka gwabaza yanmacin jiya ,a jihar Uruzghan da ke kudancin ƙasar.

Wani rikicin kuma ya ɓarke yankin Zaboul, bayan da yan taliban su ka kai harin kwanta ɓauna ga rundunar ƙasa da ƙasa a yayin da ta ke cikin sintiri.

A wata sanarwa da su ka fiddo yan taliban sun yi barazanar matsa ƙaimi wajen kai hare-hare a cikin wannan wata mai tsarki.