1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin sasanta rikicin Cote D'Ivoire

March 1, 2010

Shugaba Blais Compaore na Burkina Faso na bakin ƙoƙarinsa don ɗinke sabuwar ɓarakar da ta sake kunno kai a Cote d'Ivoire

https://p.dw.com/p/MFyA
Shugaba Omar al-Bashir da madugun 'yan tawaye Khalil IbrahimHoto: AP/picture-alliance/dpa/DW

Daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da ci gaban da aka samu a ƙasar Sudan dangane da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin gwamnati da 'yan tawayen JEM na lardin Darfur da kuma ƙoƙarin da ake yi na ɗinke ɓarakar da ta sake kunno kai a ƙasar Cote d'Ivoire. Amma da farko zamu fara ne da sharhin jaridar Berliner Zeitung a game da burin dake tattare da al'umar Nijer bayan juyin mulkin soja a makon da ya wuce. Jaridar dai cewa ta fara ne ta taɓo sharhuna na jaridun ƙasashe maƙobta kamar jaridar Sidwaya ta Burkina Faso dake cewar:"Mulkin Tanja ya faɗi kamar yadda 'ya'yan itaciya kan faɗi bayan sun nuna fiye da ƙima." A yayinda jaridar Daily Trust ta Nijeriya ke batu game da kwaɗayin mulki da kuma imanin da Tanja yayi game da cewar ba wani mai iyawa sai shi, lamarin da ya kai shi ya baro." Jaridar ta Berliner Zeitung sai ta ci gaba da cewar:

Niger Demosntration für den Militärputsch Flash-Galerie
Zanga-zangar goyan bayan juyin mulkin soja a NijerHoto: AP

"A haƙiƙa dai da a cikin watan desemban da ya wuce ne wa'adin mulkin Tanja yake ƙarewa. Amma kwatsam sai ra'ayi ya zo masa na cewar:" ai ma al'umar Nijer ba sa so ya sauka daga karagar mulki, a sakamakon haka ya canza daftarin tsarin mulkin ƙasar domin samun kafar yin ta zarce. A kuma lokacin da kotun ƙoli tayi Allah waddai da wannan mataki, haɓararren shugaban bai yi wata-wata ba wajen korar alƙalan kotun kuma jim kaɗan bayan haka ya rushe majalisar ministoci. A saboda haka matakin sojan tamkar dai mayar da martani ne akan juyin mulkin da shi kansa Tanja yayi wanda ka iya zama wani kyakkyawan mataki kan hanyar komawa ga mulkin demoƙraɗiyya tsantsa a ƙasar Nijer, kamar yadda wani masharhanci na Afirka ta Kudu ya nunar."

A ƙasar Cote d'Ivoire an shiga wani sabon hali na rashin sanin tabbas a sakamakon haka shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso ya tashi tsaye domin lafar da ƙurar rikicin tun kafin lamarin ya zama gagara-badau ko da yake su kansu sassan dake gaba da juna na tababa game da nasarar matakansa, a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta ƙara da bayani tana mai cewar:

Elfenbeinküste Präsident Laurent Gbagbo
Shugaba Laurent Gbagbo na Cote d'IvoireHoto: AP

"Ainihin musabbabin wannan sabon rikicin da shugaba Compaore na Burkina Faso ke fafutukar sasantawa shi ne matakin da shugaba Gbagbo ya ɗuka baya-bayan nan na rushe kumar zaɓe ta ƙasar Cote d'Ivoire. Tun daga wannan lokaci 'yan adawa suka ce faufau ba zasu ba da haɗin kai don kafa wata sabuwar majalisar ministoci ba, wadda ita ma aka rushe ta, suka kuma nema da a sake maido da hukumar zaɓen nan take. A dai shekara ta 2007 shugaba Copmaore ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin shugaba Gbagbo, a saboda haka a wannan karon ma sai a sa ido a ga irin rawar da zai iya takawa bisa manufa."

A wannan makon an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen JEM na lardin Darfur. A game da tasirin wannan yarjejeniya a fafutukar neman zaman kafiyar lardin na yammacin Sudan jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi tana mai cewar:

"Ko da yake yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin JEM da fadar mulki ta Khartum wani gagarumin ci gaba ne a rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a lardin Darfur kuma ta ka iya zama matakin farko na kawo ƙarshen yaƙin, lamarin da ba shakka shugaba Al-Bashir ke ɗoki da murnarsa, musamman ma dangane da rikici tsakaninsa da kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka dake birnin The Hague, amma kuma a ɗaya ɓangaren bai kamata a yi watsi da sauran ƙungiyoyin tawayen da har yau suka ƙiya ƙememe game da shiga shawarwari da gwamnati ba. Waɗannan ƙungiyoyi ka iya sanyawa murna ta koma ciki. A saboda haka har yau da sauran rina a kaba dangane da zaman lafiyar Darfur."

Mawallafi: Ahmad tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi