1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙosawar Compaore da rikicin Kot divuwar

June 2, 2010

Shugaban Burkina Faso yayi barazanar wanke hannayensa daga rikicin ƙasar Kot divuwar idan tafiyar hawainiyar ta ci gaba.

https://p.dw.com/p/Ng4R
Shugaba Blaise Compaore na Burkina FasoHoto: picture-alliance/ dpa

Shugaban ƙasar Burkina Faso yayi barazanar wanke hannayensa daga rikicin siyasar Kot divuwar, matiƙasar ƙasar ta kasa gudanar da zaɓe a wannan shekara da muke ciki. Cikin wata hira da yayi da wata kafar talabijin ta ƙasar Faransa, Blaise Compaore- ya ce zai katse duk taimakon da ya ke bayarwa -idan ƙasar ta ci gaba da burus da matakan da yarjejeniyar birnin Ouagadougou suka tanada.

Shiga tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna tsakaninsu da shugaba Compaore yayi ne, ya bayar da damar ɗinke ɓarakar da ta samu bayan yunƙurin juyin mulkin na shekara ta 2002 da ya ci tura. Shugaba Laurent Gbagbo da wa'adin mulkinsa ya shuɗe tun shekaru biyar da suka gabata- na ci gaba da ɗage zaɓen shugaban ƙasa bisa wasu matsaloli na siyasa da ke kunno kai a ƙasar ta Kot divuwar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

 Edita: Ahmad Tijjani Lawal