1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙudirin Ministocin kuɗi na duniya a taron IMF

April 25, 2010

Ministocin kudi na duniya sun yi alkawarin rage gibin kasafin kudi.

https://p.dw.com/p/N5kw
Shugaban Asusun bada lamuni na duniya IMF Dominique Strauss-Kahn, daga hagu, da kuma Youssef Boutros-Ghali, shugaban kwamitin harkokin kudi na IMFHoto: AP

Ministocin kuɗi na ƙasashen duniya sun yi alƙawarin rage giɓin kasafin kuɗi na ƙasashensu bisa laákari da matsalar ɗumbin bashi da ƙasar Girka ta tsunduma a ciki. Ministocin sun ci alwashin yin aiki tuƙuru wajen samun daidaito a yunƙurin ƙasashen duniya na farfaɗowa daga badaƙalar tattalin arziki da aka shiga. Ministocin sun yi waɗannan alƙawura ne a ƙarshen babban taron Asusun bada lamuni na duniya IMF da ya gudana jiya a birnin Washington. Ko da yake an sami saɓanin raáyi tsakanin ƙasashe masu cigaban masanaántu da ƙasashe masu tasowa a game da barazanar da ka iya tasowa dangane da matakan farfaɗo da tattalin arzikin, a ƙarshe ministocin sun amince da yin bakin ƙoƙari wajen samar da cigaban tattalin arzikin duniya. Shugaban Asusun bada lamunin na IMF Dominique Strauss-Khan ya buƙaci gwamnatoci su tabbatar da ƙarin haɗin kai a yayin da aka shiga matakin sake bunƙasa bayan matsanancin koma bayan tattalin arzikin da aka shiga a shekarar bara. A jawabin bayan taron Ministocin sun jaddada ƙudirinsu na tabbatar da ɗorewar harkokin hada hadar kuɗaɗe da kuma shawo kan matsalar bashi a tsakanin ƙasashen. A saboda haka suka buƙaci samar da wata manufa da zata dace da muradun ƙasashen don samun daidaito da ɗorewar tattalin arzikin duniya.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

  Edita      : Mohammed Nasir Awal