1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya

Halima AbbasDecember 19, 2007
https://p.dw.com/p/Cdf2

Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta zartad da wani ƙuduri dake yin kira ga cimma yarjejeniyar soke hukuncin kisa . A na zartad da wannan ƙuduri ne ƙuri’u ɗari da huɗu bisa kuri’u ishirin da tara. Ƙasar Italiya wadda ta yi magana da yawon ƙungiyar Tarayyar Turai ta ba da goyon bayanta ga wannan ƙuduri. Ƙasashen Amurka, Masar, Iran, da ƙasashen nahiyar Asiya da dama sun kaɗa ƙuri’ar nuna rashin amincewa da wannan mataki. A cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International, ƙasashe China, Iran, Iraki, Amurka, Pakistan da Sudan sune suke gudana da kashi casa’in daga cikin ɗari na kashe kashen haddi a duk faɗin duniya.