1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙungiyar Amnesty ta koka da ƙaruwar cin zarafin alúma a Afrika

May 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bux9

ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta duniya Amnesty International ta koka da ƙaruwar keta haddin alúma a wasu ƙasashe na Afrika wanda ya haɗa da kisa da kuma yiwa mata fyade. ƙungiyar ta ce ko da yake an sami raguwar rigingimu a wasu ƙasashen a bara a sakamakon yarjejeniyar sulhu da aka cimma, akwai dan ƙarfafa gwiwa a cigaban zaman lafiya da aka samu a Senegal inda yarjejeniyar da aka sanyawa a hannu a shekara ta 2004 a kudancin Casamance ta kawo ƙarshen yaƙi na tsawon shekaru ashirin a wannan yanki. Sai dai kuma a waje guda ƙungiyar ta baiyana damuwa da cigaban tashe tashen hankula a ƙasashen Burundi da Chadi da jamhuriyar dimokradiyar Congo da Cote d´Ivore da kuma Sudan, yayin da kuma a wasu ƙasashen na Afrika ake fuskantar rigingimun siyasa da rashin kwanciyar. Rahoton ya yi kakkausar suka ga gwamnatocin Afrika da tare da kungiyoyin yan tawaye a Sudan da arewacin Uganda da Chadi da Ivory Coast da kuma dimokradiyar Congo saboda cin zarafin alúma.