1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar AU za ta tura sojoji dubu shida Somaliya

July 27, 2010

Taron shugabannin Afirka ya yanke shawarar ƙara yawan sojoji a Somaliya

https://p.dw.com/p/OVOU
Shugabannin Afirka a taron AU na UgandaHoto: AP

Shugabannin ƙasashen Afirka da ke taro a ƙarƙashin lemar ƙungiyar AU a birnin Kampala na Yuganda, sun amince da ƙara yawan dakarunsu a ƙasar Somaliya. Ministan harkokin wajen Ethiopiya Seyoum Mesfin ya shedawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, taron ya amince da tura ƙarin sojoji dubu shida domin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya dake fama da hare-haren ƙungiyoyi irin su al -Shebab.

Yanzu haka dai akwai sojoji 600 da ga ƙasashen Yuganda da Burundi. A ranar 11 ga wannan watan ne dai ƙungiyar al-Shebab ta ɗauki alhakin wani harin ta'addanci da ya hallaka mutane 76 a birnin Kampala, a wani mataki da ƙungiyar ta kira shiga sharo ba shanu da Yuganda keyi a harkokin cikin gidan Somaliya.

A yau ake fatan kammala taron ƙungiyar na AU da ake gudanarwa a duk shekara wanda kuma ake fatan zai ɗauki matakan inganta tsaro da lafiya da kuma bunƙasar tattalin arziki da zamantakewar nahiyar baki ɗaya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi