1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta ɗau alkawarin ba da tallafin Euro miliyan 10 ga ’yan gudun hijiran ƙasar Lebanon.

July 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bupu

Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta yi alkawarin ba da tallfin kuɗi na kimanin Euro Miliyan 10 don taimaka wa kusan mutane dubu ɗari 5 da ke ƙaurace wa yaƙin da ake yi a Lebanon. Shugaban Hukumar Ƙungiyar Haɗin Kan Turan, Jose Manuel Barroso, ya ce tallafin zai isa a birnin London a cikin kwanaki biyu ko uku masu zuwa, kuma za a miƙa shi ne ga ƙungiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya da na sa kai. Kazalika kuma, ƙungiyar ta EU na kira ga tsagaita buɗe wuta a kudancin Lebanon, kafin a iya tura dakarun kare zaman lafiya zuwa yankin.