1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta yi marhabin da yarjejeniyar da Hamas da Fatah suka cim ma.

June 28, 2006
https://p.dw.com/p/BusQ

A wani matakin mai da martani ga ɗaukin da Isra’ila ta fara a Zirin Gazan, Ƙungiyar Haɗin Kan Turai da Amirka sun yi kira ga Isra’ilan da Falasɗinawa da su yi taka tsantsan. Babban jaim’in Ƙungiyar EUn mai kula da harkokin ƙetare, Javier Solana, ya shawarci Isra’ila da yi amfani da hanyoyin diplomasiyya wajen cim ma sako sojanta da aka yi garkuwa da shi, wanda kuma a lokaci ɗaya, yake da fasfot ɗin ƙasar Faransa. Tuni dai Faransan da Masar, sun yi ƙoƙarin shiga tsakani don sasantawa, kafin Isra’ilan ta kutsa cikin zirin Gazan.

A wata sabuwa kuma, ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta yi marhabin da wani daidaiton da aka cim ma tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa na Fatah da Hamas, wanda ya yi kira ga kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta a gefen Isra’ila. Ita dai Hamas ta ce, wannan ba yana nufin ke nan ta amince da wanzuwar Isra’ilan ba.