1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar LRA ta Uganda na ta da zaune tsaye a ƙasashe maƙobta

December 4, 2009

Rikicin tsakiyar Afirka da atsalar ɗimamar yanayi dake addabar nahiyar su ne suka fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/KqQQ
Dr. David Nyekorach Matsanga mai magana da yawun LRA a NairobiHoto: AP

A wannan makon dai rikice-rikice da suka ƙi ci suks ƙi cinyewa a ƙuryar tsakiyar nahiyar Afirka, shi ne muhimmin abin da ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus. Misali jaridar Die Tageszeitung ta yi bita akan yadda 'yan tawayen ƙasar Uganda na ƙungiyar LRA ke ci gaba da ta da zaune tsaye ba ma a Ugandan kaɗai ba, har da ƙasashen Kongo da kudancin Sudan da janhuriyar Afirka ta Tsakiya. Jaridar ta ce:

Opfer der LRA im Kongo
Wasu daga cikin waɗanda ta'asar LRA ta rutsa da su a KongoHoto: AP

"Har yau 'yan ta-kife na ƙungiyar 'yan tawaye ta LRA a ƙasar Uganda kan kai hari akai-akai a wasu ƙauyuka na kudancin Sudan dake dab da iyakokin ƙasashen Kongo da janhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda suke kashe-kashe na gilla da wawason ganima da garkuwa da mutane." Jaridar ta rawaito wata mata dake cewar: An yi shekaru ashirin ana gwabza yaƙi tsakanin arewaci da kudancin Sudan, amma ban taɓa tserewa daga yankin ba. Amma a yau bayan cimma zaman lafiya a kudancin Sudan, tilas na tsire daga ta'asar 'yan ƙungiyar LRA".

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sharhi tayi akan wani rahoto na Majalisar Ɗinkin Duniya dake nuna yadda ƙungiyar tawayen Hutu ta FDLR ke tafiyar da hada-hadar kuɗinta a sassa daban-daban na duniya. Jaridar ta ce:

"Bisa rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya dai,hada-hadar ta ƙungiyar FDLR ba kawai ta tsaya ne a ƙasar Kongo da maƙobtanta kamarsu Burundi ba, kazalika ta yaɗu zuwa Amirka da Jamus. Hakan dai yana mai yin nuni ne da cewar ba ƙungiyar ce kaɗai ke cin gajiyar wannan hada-hada ba, har ma da su kansu sojojin ƙasar Kongo dake haɗin kai a asurce da ƙungiyar FDLR da sauran ƙungiyoyi na 'yan tawaye".

Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar Majalisar Ɗinkin Duniya ɗaukar matakan da suka dace don bin diddigin ayyukan kamfanonin dake haƙar ma'adinai a ƙasar Kongo, kamar yadda jaridar Die Tages Zeitung ta nunar ta kuma ƙara da cewa:

"Fatan da masu goyan bayan wannan manufa suke yi shi ne kawo ƙarshen matakan ɗaure wa yaƙi gindi. Amma fa a ɗaya hannun akwai wasu dake ɗari-ɗari da lamarin, waɗanda a ganinsu yin hakan zai haifar da giɓi ga kuɗaɗen shigar da ƙasar Kongo ke samu daga cinikin ma'adinanta kuma al'umar ƙasar, musamman mazauna yanukunanta na gabashi su ƙara tsunduma cikin mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi".

Afirka ita ce tafi fama da raɗaɗin matsalar ɗimamar yanayi a duniya, a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai ba da la'akari da taron yanayi a Kopenhagen ta ƙasar Denmark. Jaridar ta ce:

Klimawandel Folgen Heuschrecken Mauritanien Flash-Galerie
Yaɗuwar farin ɗango sakamakon ɗimamar yanayi a AfirkaHoto: AP

"Lokaci yayi da ƙasashe mawadata zasu fara tunani a game da yadda zasu biya diyyar ɓarnar da suke wa yanayi dake haifar da matsaloli ga ƙasashe masu tasowa. Afirka dai ita ce matsalar tafi addaba, inda ɗimamar yanayi tafi ta sauran sassan duniya kuma a sakamakon haka nahiyar ke fama da bala'i daban-daban daga Indallahi. Kama daga fari zuwa ga ambaliyar ruwa da makamantansu. In har an ci gaba akan haka yawan abin da ƙasashen Afirka ke numawa zai ragu da misalin kashi 50% nan da shekara ta 2020".

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu