1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

151009 Dialogmagazin Asia Connection

February 11, 2010

Ƙungiyar Asia Connection ta matasa mawaƙan zamani ne a ƙasar Turkiya

https://p.dw.com/p/LyeV
Hoto: Nigel Parry

Wata ƙungiyar mawaƙan zamani na salon rap ko kuma Hiphop daga ƙasar Turkiya da ake kira Asia Connection, matasa ne musulmai suka kafa ta, kuma sun shahara saboda salon waƙoƙin da suke yi suna haɗawa da kalmomi na addinin musulunci. A kullum yawan masu sha´awar waƙoƙinsu na ƙaruwa, haka kuma masu sukar lamirinsu da suka haɗa da musulmi da waɗanda ba musulmi ba. Shirin na yau ya samu zantawa da ´ya´yan wannan ƙungiya ta mawaƙan zamani daga ƙasar Turkiya.

Kadikoy wani yanki ne na ɓangaren Asiya dake birnin Istanbul na ƙasar Turkiya. A wata ƙaramar hanya da ta ƙunshi gidajen abinci da shan shayi ko gahawa a yankin an yi zanen wani hoto da ka yiwa taken “Taimakon gaggawa.”

Daga wani shago dake dab da wannan zanen ana jin sautin waƙoƙin zamani salon Hip Hop na Turkiya, an rataya mutum mutumi daban daban da dogayen rigunan T-Shirt da wandunan zamani ana sayarwa. Wannan yanayin ba safai ake gani a titunan birnin Istanbul ba. Mawaƙan zamani na Hiphop kamar Süphe wanda tsawon T-Shirt dinsa ya wuce guiwa, suna ɗaukar hankali a irin waɗannan wurare.

“Ina zuwa sallar juma´a akai akai, wani lokaci in kan je sanye da ´yan kunne sannan abokai na kuma suna da shasshawa a jikinsu. Sauran mutane na yi mana wani irin kallo sai ka ce mu wasu dodanni ne. Ina jin da za su fi son su ga wasu musulmai daban a masallatai.”

A kowace rana Süphe na zuwa unguwar Kadikoy inda yake haɗuwa da sauran mawaƙan Hiphop. Kimanin shekara guda kenan da ya kafa ƙungiyar Asia Connection. Kasancewarsa mutum ne mai ra´ayin addini, waƙoƙin rap ko hiphop da Süphe ke rerawa sun banbanta da na sauran mawaƙa irinsa.

“Ni musulmi ne saboda haka ka da ka ji tsoro. Ina bin dokokin addinin Musulunci sau da ƙafa.”

Wani abokin hulɗarsa shi a sanye da wandon wasan motsa jiki da abin jin sauti a ka, ya kan je shagon a unguwar Kadikoy. Sunan wannan aboki na Süphe a fagen waƙa, Radikal wato mai tsaurin ra´ayi. Da yake gabatar da kansa Radikal ya shafa saje da gemunsa na musulunci yana mai cewa a rayuwasa a da ya rarrabe tsakanin addini da waƙoƙin hiphop, amma yau sun zama abu ɗaya. 

“Ina sauraran waƙoƙin “rap” musamman na Faransanci. Da yawa daga cikin mawaƙan rap na Faransanci, musulmai ne masu asali da ƙasashen Larabawa. Sau da yawa suna fara waƙoƙinsu da kalmomi kamar “Bismillahi” ko wasu ayoyi na Al-Kura´ani mai girma. Na yi tunani cewa mai zai hana ni ma in yi ƙoƙarin kwaikwayonsu?”

A cikin shekara ta 2008 Radikal da Süphe sun yi haɗin guiwa suka rera faifayen su na farko na salon hiphop mai ƙunshe da kalmomin addinin musulunci.

“Da farko mun yi niyar yin waƙoƙi guda 12 amma sai muka tsorata saboda martanin da aka samu daga jama´a. A ƙasar Turkiya kowa na da ´yancin yin addininsa ba da wata tsangwama ba. Amma ba mu san yadda aka samu haɗaka tsakanin addinin Musulunci da salon waƙoƙi daga ƙetare ba. Mun ji tsoro ka da a yi mana mummunar fahimta.”

A ƙarshe faifayen ya ƙunshi waƙoƙi guda uku da ake iya jinsu ta yanar gizo musamman ta hanyoyin sadarwa na Myspace da YouTube. 

“Na kan samu saƙonnin Emails ko ta hanyar Facebook ko Myspace. Dukkansu kalma guda suke yi wato: “Allah Yayi maka albarka, muna sauraron waƙoƙinka wani lokaci tare da iyalinmu da iyayenmu”. Ina matuƙar alfahari da haka.”

Da ma masu iya magana kan ce kazar wani angulun wani. Yayin da wasu ke sha´awar waƙoƙin wasu kuwa ƙyamar su suke yi. Ba dukkan martanin da ake mayarwa game da ƙungiyar ta Asia Connection ke da kyau ba, musamman daga ɓangaren addini inda a kullum ake sukar wannan ƙungiya, inji Radikal sannan sai ya ƙara da cewa.

“Alal misali wani ya taɓa rubuto min saƙo a Myspace yana mai cewa: “Kana iƙirarin cewa kai musulmi ne kuma kana rera waƙoƙin rap na musulunci. Ba kan san babban zunubi ne rera irin waɗannan waƙoƙi ba? Yayi ƙoƙarin kare kansa da wasu ayoyi daga al-Kur´ani mai girma. To amma gaskiya muna ƙoƙari mu yi watsi da masu irin wannan ra´ayi, in ba haka ba za mu iya zama a Turkiya ba.”

Wani nazari da masu ilimin halayyar zaman jama´a da masana kimiyyar siyasa suka gudanar sun gano cewa tun bayan 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 yawan matasa a ƙasar Turkiya da ma a sauran ƙasashen Musulmi suna karkata ga addinin Musulunci, suna fitowa fili suna nuna cewa su Musulmi ne. Ita ma ƙungiyar Asia Connection da salon waƙoƙinta na rap wannan manufa ta sa gaba. A kullum yawan masu sha´awar waƙoƙinta sai ƙaruwa ya ke saboda kalmomi na addini. Shin ko saboda neman kasuwa take bin wannan salo? Süphe ya yi ƙarin bayani kamar haka. 

“Allah ne shaida na, wallahi ba ina yi ne don neman suna ba. Ina waƙa ne yadda na ke jin daɗin ta. Ka san Annabi ya umarce mu da mu yaɗa addinin Musulunci. Ya umarce mu da mu koyi addinin kuma mu yaɗa shi. Allah Ya yi min baiwa ta iya ma´amala da mutane. Wannan kuwa abu ne mai kyau idan daga cikin mutane dubu 10 zan iya shawo kan ɗaya ya yi sha´awar addinin kuma ya musulunta.”

Yanzu dai kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu domin a ƙarshen shekara Asia Connection ta fid da faifayenta na biyu, wannan karo a ɗakin ɗaukar sauti amma ba a falon wani aka ɗauka ba.

Mawallafa: Luise Sammann/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal