1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar NATO ta karɓi jagoranci dakarun ƙasa da ƙasa a Afghnistan.

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoQ

A yau ne ƙungiyar NATO za ta fara jagorancin rundunar dakarun ƙasa da ƙasa da aka girke a Afghanistan. Wannan kuma, shi ne karo na farko da ƙungiyar za ta shiga cikin wani yaƙi da ake yi a ƙasa. Rundunar da NATOn za ta jagoranci dai, ya ƙunshi dakaru ne daga Birtaniya, da Kyanada, da kuma Holland. Da can dai dakarun Amirka, waɗanda suka hamɓarad da gwamnatin Taliban a cikin shekara ta 2001 ne ke jagorancin rundunar.

Masharhanta kan harkokin ƙungiyar ta NATO sun ce wannan aikin shi ne zai fi ƙalubalantarta, a tarihinta na shekaru 57 da suka wuce.

Dakarun NATOn dai na girke ne yankunan kudancin Afghanistan, inda ’yan ƙungiyar Taliban ke da ramin kurarsu da kuma magoya baya. A ɗauki ba daɗin da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu a kwanakin bayan nan dai, ƙungiyar NATOn ta yi asarar dakarunta da dama.