1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Tarayyar Afirka na angaza wa ’yan tawayen Darfur don su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

May 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuyK

Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, ta yi barazanar neman Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya wa ƙungiyoyin ’yan tawayen Darfur guda biyu takunkumi, idan suka ƙi sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnattin birnin Khartoum. Kawo yanzu dai, babbar ƙungiyar ’yan tawayen Darfur ɗin ce kawai ta sanya hannu kan yarjejeniyar, don kawo ƙarshen yaƙin basasa da ya janyo asarar rayukan dubannin mutane da kuma tilasa wa jama’a fiye da miliyan biyu yin ƙaura daga matsugunansu. Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya ce kamata ya yi a maye gurbin dakarun Ƙungiyar AU cikin gaggawa, da na Majalisar, don gudanad da ayyukan kare zaman lafiya a yankin na Darfur. Kofi Annan ya kuma yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da ta ba da taimakon agaji don a iya shawo kan abin da ya kira wannan bala’i mafi muni da ya taɓa shafan jinsin bil’Adama.