Ƙungiyar 'yan adawa a ƙasar Ethiopia ta yi watsi da sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki
May 26, 2010Talla
Ƙungiyar yan adawa a ƙasar Ethiopia ta yi watsi da sakamakon zaɓuɓukan yan majalisun dokokin da aka gudanar a ranar lahadin da ta gabata ,wanda jam'iyyar Shugaban ƙasar Meles Zenawi ta samu gagarumin rinjaye a kai.Da ya ke magana da kamfanin dilancin labarai na Faransa AFP wani jagoran yan adawar Merara Guidina ya shedda cewa ko ƙaɗan ba zasu amince da sakamakon zaɓen ba, sanan kuma ya ce za su matsa ƙaimi domin a sake shirya wani sabon zaɓen.Wannan sanarwa ta yan adwar ta zone a daidai lokacin da masu saka ido a zaɓen na ƙungiyar tarayya Turai suka ce zaɓen ya na cikke da kura kurai.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita Umaru Aliyu