1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ’yan tawayen Darfur ta yi watsi da wa’adin da aka sanya mata.

May 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuwJ

Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ’yan tawayen yankin Darfur, ta ce duk da ƙaratowar ranar cikar wa’adin da aka ba ta, ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a yankin na yammacin Sudan, ba za ta shiga yarjejeniyar ba, sai an yi mata kwaskwarima.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU dai, ta yi barazanar sanya wa duk ƙungiyoyin ’yan tawayen yankin Darfur ɗin takunkumi ne, idan ba su sanya hannu suka kuma amince da yarjejeniyar da aka cim ma a ran 5 ga wannan watan tsakanin gwamnatin Sudan da babban reshen ƙungiyar ’yan tawayen ta SLA ba. A halin yanzu dai, ƙungiyar JEM da kuma wani reshe na ƙungiyar SLA ne barazanar ta shafa.

Shugaban ƙungiyar JEM, Khalil Ibrahim, ya faɗa wa maneman labarai a birnin al-Ƙahira cewa, zai halarci wani taro a ƙasar Sloveniya gobe talata, inda za a yi ƙoƙarin cim ma wata madafa tsakanin ƙungiyoyin da ke watsi da yarjejeniyar da kuma Ƙungiyar AU. Ya ƙara da cewa, muddin ba a tabbatar wa yankin na Darfur gwamnatinta ta jiha ba, ba a kuma tsara shirye-shiryen sake gina yankin, da biyan mazaunan da aka ci zarafinsu diyya, da ba su damar riƙe madafan iko ba, to fa ƙungiyarsa ba za ta amince ko kuma sanya hannu kan yarjejeniyar ba.