1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyoyin agaji sun ce yawan baƙin hauren da suka rasa rayukansu a tsibirin Canaries na ƙara haɓaka.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bukx

Ƙungiyoyin ba da taimamkon agaji sun ce yawan baƙin hauren da suka rasa rayukansu, a yunƙurinsu na isa tsibirin Canaries a ƙarshen makon da ya gabata, ya ƙara haɓaka. Kawo yanzu dai rahotanni na nuna cewa an tsamo gawawwaki 84 na baƙin hauren daga teku, yayin da har ila yau ba a san makomar wasu baƙin hauren guda 50 ba tukuna. A ran asabar da ta wuce ne, wasu jiragen ruwa ɗauke da baƙin haure daga Murteniya suka nitse a gaɓar tekun tsibirin Canaries, yayin da tsakanin jiya da yau kuma aka kame wasu ɗari biyu da hamsin, waɗanda ke yunƙurin isa a tsibirin. Ƙasar Spain, mai mallakar tsibiran na Canaries, ta yi kira ga Ƙungiyar EU da ta tallafa mata, wajen shawo kan ambaliyar baƙin hauren da take huskanta.