1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyoyin kare hakkin bil adama sun soki rikicin Tchadi

Yahouza, SadissouFebruary 29, 2008

Taɓarɓarewar ´yancin bani adama a Tchad na tada hankulan jama´a.

https://p.dw.com/p/DFUn
Rikicin tawaye a TchadHoto: AP


Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama na ci gaba da bayyana damuwa a game da halin taɓarɓarewar ´yancin jama´a a ƙasar Tchad.


Taɓarɓarewar ´yancin da walwalar jama´a a ƙasar Tchad ta fuskanci mummunan koma baya tun harin baya bayan nan da ´yan tawaye suka kai a birnin N´Djamena da zumar kifar ada shugaba Idriss Deby Itno.

Tun daga wannan lokaci gwamnati ta shiga kamun kan mai uwa da wabi.

Wannan cafke cafke ya rutsa da wasu shugabanin jam´iyun adawa na ƙasa , daga cikinsu akwai Ibni Umar Mahamat Saley da kuma Ngarlegy Yorongar, wanda har ya zuwa yanzu a ka samuzn ɗuriyar su.

Ƙungiyoyin fara hulla sun ɗora alhakin ɓacewar wannan ´yan adawa ga gwamnati.

Patrice Bendunga shugaba ne na haɗin gwiwar Ƙungiyoyin yaƙi da tozarci da kuma neman zaman lafia a Tchad wanda kuma a halin yanzu ke a nan birnin Bonn ya bayyana yadda ake ciki yanzu a Tchad.

A jiya shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy dake bada haɗin kai ga gwamnatin Idris Deby ya kai ziyara aiki a ƙasar Tchad inda ya tattana da hukumomin ƙasar a game da wannan baddaƙala, Patrice Bendunga yayi tsokaci agame da yaunin da ya rataya kan France wajen warware rikicin Tchad.

Albarkacin wannan ziyara da shugaba Sarkozy ya kai a birnin N´Djamena an gudanar da taro tsakanin wakilan gwamnati da na Ƙungiyoyin fara hula to saidai a cewar Bendunga wannan taro ba shi da wani tasiri.

A halin da ake ciki, bisa matsin lambar ƙasashen ƙetare hukumomin Tchad sun amince su girka wani komitin bincike na ƙasa da ƙasa wanda zai gano haske a game da ɓacewar ´yan adawar guda biyu, to saidai a cewar Ƙungiyoyion fara hulla wakilan gwamnatin ƙasar France da na Tchad za su kasance a matsayin wanda aka yi sata tare da su, sannan kuma a koma biya sau tare da su.