1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyoyin ’yan ta kifen Falasɗinawa sun lashi takobin ɗaukar fansa kan Isra’ila.

June 21, 2006
https://p.dw.com/p/But2

Wasu ƙungiyoyin ’yan ta kifen Falasɗinawa sun lashi takobin mai wa Isra’ila martani dangane da harin da jiragen saman yaƙinta suka kai a zirin Gaza, inda yaran Falasɗinawa 3 suka rasa rayukansu, sa’annan mutane 14 kuma suka ji rauni. Jami’an Isra’ilan dai sun ce sun kai hari a zirin Gazan ne a kan wasu Falasɗinawa, waɗanda ke da hannu wajen harba rokoki zuwa ƙasar bani Yahudun. Sai dai, Falasɗinawan sun sami tserewa kafin bamabaman da jiragen yaƙin Isra’ilan suka jefa musu su tashi.

A makon da ya gabata ma, sai Isra’ila ta kai irin wannan harin a zirin Gazan, inda fararen hular Falasɗinawa guda 8, da wasu mayaƙn ƙungiyoyin Falasɗinawan guda biyu suka rasa rayukansu.

Ita Isra’ila dai ta bayyana nadamarta game da asarar rayukan fararen hular Falasɗinawan. Sai dai ta kuma ce shugabannin Falasɗinawan ne ke ɗauke da nauyin duk abin da ke wakana, saboda gazawarsu wajen hana ’yan ta kife harba rokoki zuwa harabobinta.