1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙura ta laffa a birnin Conacry na Ƙasar Guinee

June 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuuC

A birnin Konakory na ƙasar Guine, ƙura ta laffa bayan rigingimmun da su ka ɓarke jiya,, tsakanin yan sanda, da ɗallibai, wanda kuma su ka yi sanadiyar mutuwar mutane 10.

Kakakin gwmantin kasar Musa Solana, ya bayyana takaicin abukuwar wannan haɗari.

Ya kuma zargi jam´iyun adawa, da shirya maƙarƙashiyar tada zaune tsaye cikin ƙasa, ta hanyar anfani da yan makaranta.

A ɗaya hannun kuma, ƙungyiyoyin ƙwadagon ƙasar, na ci gaba da yajin aiki, irin na sai inda mai ƙare .

Sun fara wannan yaji, tun ranar alhamis da ta gabata, su na masu buƙatar gwamnati, ta biya masu buƙatocin su da su ka haɗa da albashi,da sauran harakoki na more rayuwa.