1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙyamar jinsi na neman sake kunno kai a Afirka ta Kudu

April 7, 2010

Cibiyar nazarin harkokin cikin gida ta Afirka ta Kudu ta wallafa wani rahoto da ke nuna yadda wariyar launin fata ta ke daɗa yaɗuwa a ƙasar.

https://p.dw.com/p/MpgY
Yaƙi da wariyar launin fata.Hoto: picture-alliance/ dpa

Ita wannan cibiya da ɗan uwan tsohon shugaba Thabo Mbeki ke shugabanta, ta nunar da cewa abin takaicinma shi ne, aƙalla kashi 40 daga cikin 100 na jinsunan Afirka ta kudu na ci gaba da yi wa junansu kallon hadarin kaji. kana sama da rabin su yan ƙasar ba sa cunɗaya tsakaninsu a hada-hada ta yau da kullum. Maimakon haka ma, ana ci gaba da samun unguwannin ya ku bayi da baƙaƙe zalla ne ke da zama a ciki, da kuma ungawannin masu hannu da shuni na manyan manoma fararen fata. Shugaban cibiyar nazarin harkokin na Afirka ta kudu ya fito fili ya zargin gwamanti da haddasa wannan ƙyama tsakanin baƙaƙe da fararen fata.

"Ya ce jam´iyar da ke mulki ba ta cika alƙawurin samar ma yan ƙasa ƙarin ƙuɗin shiga ba kamar yadda ta alƙawarta shekaru 16 da suka gabata. A saboda haka ne ANC ta kenam wanda za ta ɗora ma alhakin gazawa da ta yi. A ganinta kuwa, manoma fararen fata ne suka haifar da karar tsaye ga muradunsu na tattalin arziki."

Kolonialismus Afrika Südafrika Farm Arbeiter
Baƙaƙe na ci gaba da aiki a gonakin fararen fata.Hoto: picture alliance/imagestate/HIP

Sai dai wasu na ganin cewa idan aka kwatanta da shekarun da ƙasar ke dare gida biyu, da ci gaba mai ma´ana da aka samu a fannin zamantakewa tsakanin baƙaƙen na Afirka ta kudu da kuma fareren fata. Ko wannan jam´iya da Terreneuve ya ke jagoranta, kusan an daina jin ɗuriyarta a fagen siyasar ƙasar ta Afirka ta kudu, domin ba ta da waɗanda aka zaɓa ƙarƙashinta. Shugaban gidan ajiyan kayan tarihi da ke da nasaba a zamanin ƙyamar jinsi, wato Christopher Till na ganin cewa ko tsakanin matasa baƙaƙe da farare ya isa misali.

"Ya ce a makarantunmu cuɗanya tsakanin jinsi ta fara samun gindin zama. Muna alfahari idan muka ga ɗalibai baƙaƙe da fararen fata sun jera tare domin ziyartar gidan ajiyan kayan tarihi na ƙyamar jinsi. matasan dai sun fi samun fahimta tsakaninsu fiye da iyayensu da suka girma a cikin yanayi na kallon hadarin kaji."

Rahoton cibiyar da ɗan uwan Thabo Mbeki ke shugabanta ya nunar da cewa matiƙar ba a rage makeken giɓi da ke tsakanin baƙaƙe da fararen fata a sigar samun kuɗin shiga ba, to lallai ba za a rabu da Bukar. Dama ƙididdiga ta nunar da cewa a jimilce a dadadin kuɗi da ke shiga aljuhun kowani farar fata na Afirka ta kudu na ninka so bakwai adadin masu gida rana da ke shiga aljuhun baƙar fata. Alhali ficeccen ɗan ƙasar wato Nelson Mandela ya sadokar da kansa domin tabbatar da cewa wannan wariya da ƙyama da rashin fahimtar juna sun kau a Afirka ta kudu. Ko lokacin da ya fito daga gidan yarin ƙare kukanka a shekara ta 1990, manufofinsa ba su sauya ba.

Nelson Mandela und Friedrich de Klerk erhalten Friedensnobelpreis
Lambar Nobel ta Mandela da Declerk bayan kawar da ƙyamar jinsi.Hoto: AP

"Mandela ya ce na sadokar da rayuwata domin inga an kawo ƙarshen tursasawa da ake nunama baƙaƙe.na yi imanin cewa baƙaƙe da fararen fata za su iya yi rayuwa kafaɗa da kafaɗa da juna."

Afirka ta kudun dai, na ci gaba da ɗaukan matakan da zai raba jinsunan ƙasar da ƙyamar junansu. Tuni ta gurfanar da baƙaƙen biyu da ake zargi da kashe Terre Blanche a gaban ƙuliya domin jan birki ga masu son mai da ƙasar kan turbar ƙyama da wariya da ta fiskanta a baya.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita:Halimatu Abbas