1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓarin wuta a Nahr Al-Bared

August 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuEm

A matsugunin yan gudun hijira na Nahr Al bared dake arewacin ƙasar Libanon a naci gaba da ɓarin wuta, tsakanin dakarun gwamnati da yan takifen Fatah Al Islma.

A cewar kakakin sojojin gwamnatin Libanon,ya zuwa yanzu saura kiris su fattataki yan takifen daga yankin bakin ɗaya.

To saidai a yammacin yau ma, ƙarin soja ɗaya na Libanon ya rasa ran sa, a cikin wannan faɗa.

Tun daga farkon wannan rikici ranar 20 ga watan mayu da ya gabata zuwa yanzu, mutane 200 su ka rasa rayuka a cikin arangama, wanda su ka haɗa da sojoji fiye da 130 na gwamnati.

Mutane kimanin dubu 40 da ke zaune a wannan yankin sun fice domin tsira da rayuka.

Praministan Libanon Fouad Siniora, ya tabbatar da cewa, dakarun sa, za su ci gaba da darkakawa, har sai sun kakkaɓe yan takifen Nahr AL bared, wanda su ka nuna turjewa mai tsanani.