1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗiyan riƙo a Afirka

August 5, 2009

Yaro na kowa ne ga al´adar ƙasashen nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/J41B
Hoto: DW

Al'umar ƙasashen Afirka musanman a nan yanmacin Afirka, mukan ɗauki yaro tamkar ɗan kowa. Idan ka ga yaro kan hanya yana shaiɗana ko kuma yana aikata wani abinda bai kamata ba kai a matsayin babba kana da damar yi masa faɗa ko da baka san shi ba ko ma gidan da ya fito ba. Haka kuma idan namiji ya rabu da matarsa ko ta hanyar mutuwar aure ko kuma Allah Ya yiwa matar rasuwa, sai ya ƙara aure, to yayi wannan aure ne da muhinman dalilai guda biyu. Na farko ya cika ƙa'idar aure kamar yada addini ya rataya masa, na biyu kuwa ya samarwa yaransa uwa.

Yau shirin Abu namu zai duba irin nauyin da ya rataya a wuyar wannan baiwar Allah game da tarbiyar da 'ya 'yan miji da kuma shi namijin da ya auri mata mai ɗa daga wani gidan.

Marubuciya: Rabi Abubakar Gwandu

Edita: Mohammad Awal