1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano matsalolin Lantarki a Najeriya

February 7, 2017

Taron koli a kan harkar wutar lantarki tsakanin majalisar dokokin Najeriya ya bankado matsaloli da ke haddasa koma baya a fannin, duk da makuddan kudadden da aka kashe tare da sayar da wasni sahi ga ‘yan kasuwa.

https://p.dw.com/p/2X8JO
Elektrizität Afrika
Hoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Nigeria Strom Konf - MP3-Mono

Kwararu a fanin wutar lantarki a Najeriyar da ‘yan majalisar dokoki da bangaren zartaswa sun yi kokarin fadawa juna gaskiya game da harkar samar da wutar lantarkin Najeriyar da a kullum ke zama gwamma jiya da yau, saboda dukkanin alkawura na samun ingantuwar wutar na neman zama tamkar tatsuniyar da ‘yan Najeriyar suka gaji da ji.

An dai bankado matsaloli da suka sanya mafi yawan jama'a yin tagumi da ma girgiza kai a game da halin da harkar wutar lantarkin Najeriyar ke ciki, abinda ya sanya shugaban majalisar wakilan Najeriyar Hon Yakubu Dogara cewa  ba zai lamunci yadda aka kashe Naira tiriliyan 2.7 a fanin wutan lantarkin ba,ba tare da wani ci gaba ba. Ko akwai wani abu sabo da suke shirin yi a yanzu.

Elektrizität Afrika
Tashar wutar lantarki a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Shekaru shida bayan da Najeriyar ta mayar da sashin lantarkin a hannun ‘yan kasuwa babu wani ci gaba mai ma'ana, koda a wannan shekarar sau uku ana samun rushewar daukacin tsarin  daga megawatt dubu 4 yakan koma kasa da dubu guda. To sai dai ga Injinya Joe Makoju tsohon shugaban hukumar samar da wutar da aka cefanar da ita a kasar yace tun farko aka samu matsala  domin babu kasar da ke sayar da daukacin kamfanoninta, don an tsara a fara sayar da wasu a matsayin gwaji amma aka yi watsi da lamarin yana mai cewa:

''Matsala ta farko itace  wadanda suka shiga lamarin sun jahilci daukacin tsarin samar da wutan lantarki a Najeriya wanda muhimmin lamari ne, don haka sai kawai aka cusa son rai a cikin daukacin lamarin sayar da kamfanonin, babu wani fitaccen kamfani da aka san shi a harkar nan da ya samu. An ki bin shawarar da aka bayar ta a fara da wasu sassa a matsayin gwaji ba wai sayar da daukacin sashin ba"

Solaranlagen in Südnigeria
Allunan samar da wutar lantarki ta hasken ranaHoto: Johan Demarle & Damon van der Linde

A yayinda kamfanonin samar da wutar ke  korafi na rashin iskar gas ga na'urorinsu bayan zargin nuna waka sani wajen sayen kamfanonin da aka ma bisu da Karin tallafi na milyoyi. Duk da fata ta samun ci gaba musamman batun samar da wutan lantarki ta hanyoyin zamani na hasken rana da iska, da alamun sarkakiyar da ke cikin harkar wutan lantarki Najeriyar na da wuyan fahimta, domin a shekaru 56 Najeriyar bata iya zarta samar da megawatt dubu biyar ba za'a sa ido a gani shin shigar da sashin majalisa ya yi zai kawo wani canji a kasar da mafi yawan al'ummarta ke rayuwa cikin duhu na rashin wutan lantarki? Lokaci ne zai nuna hakan.