1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

[No title]

September 30, 2010
https://p.dw.com/p/POV4
Superteaser 20 Jahre Eins Hausa

A ranar uku ga watan oktoban shekara ta 1990 Jamusawa suka yi bikin sake haɗewar ƙasarsu bayan rarrabuwa ta tsawon shekaru 45. Jim kaɗan kafin haka katangar Berlin ta rushe. To sai dai kuma babban aikin da ya kasance a gaba shi ne yadda za a mayar da ƙasashe biyu da suka banbanta da juna ƙarƙashin tuta guda tamkar ƙasa ɗaya al'uma ɗaya. Shekaru 20 bayan haka Deutsche Welle ta yi bitar sakamakon lamarin domin tantance yadda 'yan gabaci da 'yan yammaci ke tafiyar da rayuwarsu a yau. Shin a wani ɓangare ne haɗin kan ya tabbata kuma a ina akwai sauran rina a kaba? Kuma shin mene ne muhimmancin haɗewar ga waɗanda ba su da wata masaniya game da rarrabuwar?