1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

11-2001 / 11-2007 shekaru 6 kenanda kai hare-haren ƙunar baƙin wake mafi muni a dunia a ƙasar Amurika

September 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuBd

Kaɗan kenan daga addu´o´in da ɗaruruwan mutane su ka yi, a birnin New York na ƙasar Amurika, albarkacin cikwan shekaru 6, da hare-haren ta´adancin da su ka rutsa da ƙasar.

Kwana ta shi, yau shekaru 6 kenan daidai da wasu yan takife su ka kai hare-hare ga tagwayen benayen birnin New York , wanda ke matsayin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta dunia.

A baki ɗaya mutane 2.993 su ka rasa rayuka a cikin wannan hare-hare, wanda bayan New York, su ka shafi Washington, da Pennsylvania.

Kamar ko wace shekara, magajin garin New York Michael Bloomberg, ya nuna alhini ga mamantan sannan, an kiri sunayen su ɗaya bayan ɗaya.

Tun daga ranar 11 ga watan satumber na shekara ta 2001, ƙasar Amurika ta tsaurrara matakan tsaro, ta kuma ƙaddamar da yaƙi da ta´adanci da yan ta´ada a dunia.

Albarkacin cikwan shekarun 6, Usama Bin Laden shugaban ƙungiyar Al´qida, wada ta ɗauki alhakin kai wannan hare-hare, ya gabatar da saban jawabi na Video a yau talata.

Ben Laden, ya yi yabo na mussamman ga matuƙin jirgin da ya jagorancin hare-haren na Amurika, sannan ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙar Amurika, da sauran ƙasashe, yan amshin shatan ta, wanda a cewar sa, su ka ɗaura ɗamara yaƙi da musulunci.