1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aƙalla mutane 64 sun rasu a wani hari da aka kai kan jirgin ƙasa a Indiya

February 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuRR
Fiye da mutane 64 sun rasu sannan wasu da ba´a san adadin su ba sun jikata a wani harin bam da aka kai kan wani jirgin kasa dake kan hanya daga jihar Haryana dake arewacin Indiya zuwa kasar Pakistan. Daukacin wadanda harin ya rutsa da su ´yan Pakistan ne. Ministan sufurin jiragen kasa Lalu Prasad ya ce an dana bama-baman ne a cikin taragu biyu na jirgin. Ministan ya ce da hannun masu matsanancin kishin Islama a harin, wanda ya ce wani yunkuri ne na yiwa shirin zaman lafiya tsakanin Indiya da Pakistan yankan baya. A cikin kwanaki masu ake sa ran isar ministan harkokin wajen Pakistan Mian Khursheed Mahmud Kasuri a Indiya, inda zai tattauna da takwaransa na wannan kasa.