1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A gobe ne zaa bude taron tattauna na WTO a Geneva

January 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuT3

Manyan kasa masu arzikin masanaantu na duniya sun amince da koma teburin tattaunawa dangane da sakarwa harkokin kasuwanci mara,batu da aka dakatar tun a watanni shida da suka gabata,lokacin da kasashe matalauta akarkashin jagorancin kasar Brazil suka samu sabanin raayi da Amurka da kasashen kungiyar turai.A taron da suka gudanara abirnin Davos din kasar Switzerland,ministocin harkokin ciniki na kasashe 30 sun bayyana tabbacinsu na sake komawa wannan tattaunawa.Premien Britani Tony Blair,yace akwai dukkan alamu dake nuni dacewa zaa cimma tudun dafawa adangane da wannan tattaunawa.A DANGANE DA HAKANE AKESARAN BUDE TARON WAKILAI A birnin Geneva agobe litinin idan mai duka ya kaimu,inda ke zama cibiyar kungiyar ciniki ta duniya,inda kuma zasu tattauna zagayen tattaunawar Doha ,data sha fuskantar matsaloli a baya.