1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Indonesiya, ana ta ƙara samun yawan waɗanda suka rasa rayukansu a girgizar ƙasar da ta addabi tsibirin Java a ran asabar da ta wuce.

May 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuwF

Alƙaluman baya-bayan nan da hukumar Indonesiya ta buga na nuna cewa, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a girgizar ƙasar da aka yi a kan tsibirin Java, a ran asabar da ta wuce, ya tashi zuwa dubu 5 da ɗari ɗaya. A halin da ake ciki dai, Majalisar Ɗinkin Duniya, da Ƙungiyar Red Cross ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Geneva na ƙasar Switzerland na ta ƙoƙarin kai taimakon agajin da aka samu daga gamayyar ƙasa da ƙasa, zuwa yankin cikin gaggawa.

Jami’an ceto kuma na nan na ta ƙokartawa don agaza wa jama’a a birnin Jok-Jakarata, inda girgizar ta fi muni, inda kuma kusan mutane dubu ɗari biyu ne aka ƙiyasci cewa sun rasa matsugunansu.

Shugaban ƙasar Indonesiyan, Susilo Bambang Yudhoyono, ya bayyana farin cikinsa ga yadda ake ta kawo taimako daga wasu yankunan ƙasar da kuma ƙetare, zuwa yankunan da bala’in ya shafa:-

„Akwai tawagar da ta iso jiya daga Singapore. A cikin tattaunawar da na yi da sauran shugabannin duniya kuma, sun tabbatar mini da shirinsu na taimaka wa Indonesiya, a wannan mawuyacin halin da ta sami kanta a ciki. Ina bayyana matuƙar godiyata ga hakan. Kuma ina farin cikin ganin cewa ’yan ƙasarmu ma na ba da tallafi da kuma agaza wa ’yan uwansu, waɗanda a halin yanzu ke cikin wani mawuyacin hali.“