1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A mako mai zuwa shugaba Bush zai gana da Firaminista Maliki a Jordan

November 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buaq

Shugaban Amirka GWB da FM Iraqi Nuri al-Maliki zasu yi wata ganawa ta ba zata a Amman babban birnin kasar Jordan a cikin makon mai zuwa, inda zasu tattauna game da harkokin tsaro a Iraqi. A cikin wata sanarwa da fadar White House ta bayar, shugabannin biyu zasu shawarta game da mikawa Iraqi aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya. Hakazalika Bush da al-Maliki zasu kuma gana da sarkin Jordan Abdullah na biyu. Shugaba Bush zai kaiwa birnin Amman ziyara ne bayan taron kolin kungiyar tsaro ta NATO wanda za´a yi a Riga, babban birnin Latvia.