1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A na ci gaba da ɓarin wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah

August 10, 2006
https://p.dw.com/p/BunC

A ƙasar Sri Lanka ana ci gaba da gabazawa tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye Tamoul Tigers.

Rahotani daga Colombo babban birnin ƙasar sun ruwaito cewa da sanhin sahiyar yau sojoji 23 masu biyyaya ga gwamnati su ka ji mummunan raunuka a cikin wannan yaƙi.

An yi ɓarin wutar na yau ,a kussa da madatsar ruwan Maavilaru da ke arewa maso gabacin ƙasar wanda kuma yan tawaye su ka kame har tsawan kussan sati 3.

A tsukin wannan lokaci, mutane 440 su ka rasa rayuka a yaƙin da aka gwabza tsakanin ɓangarorin 2.

Bayan yan tawaye sun bayana hita daga madatsar ruwan al´ummomin ƙasar, sun tsamaci lafawar ƙura, amma hakan ba ta samu.

Ministan harakokin wajen Sri Lanka, Samaraweera ya bayyana cigaban yaƙin a matsayin wani mataki na kakkaɓe yan tawayen daga ƙasar: ya ce

„Wannan sakamakon alƙiblar da gwamnati ce, ta sa gaba ta yaƙar mummunan ayyukan ta´adanci da ke wakana a ƙasar mu.

Yanzu kuma, mu na buƙatar sai mun ga bayan wasu yan tsirarun shugabanin tawayenTamouls Tigers, wanda kwata kawata basu san ba mine demokadiya.“

Yaƙe- yaƙen na abkuwa, a yayin da ake ci gaba da bincike, domin gano mussababin mutuwar jami´ai 17 na ƙungiyar bada agaji, ta France, Action contre la Fin, wanda a ka sami gawwawakin su ranar litinin da ta wuce.